Babu wani laifi ko rashin dacewa don ka roki a yi following dinka a Facebook – Comr Abba Sani Pantami2024

Shugaban kamfanin ABBA PANTAMI DATA, Comr Abba Sani Pantami ya bayyana haka ne a shafin sa na Facebook don karfafawa masa Giwa

Spread the love

Shugaban kamfanin ABBA PANTAMI DATA, Comr Abba Sani Pantami ya bayyana haka ne a shafin sa na Facebook don karfafawa masa Giwa

Babu wani laifi ko rashin dacewa don ka roki a yi following dinka a Facebook - Comr Abba Sani Pantami2024
Comr Abba Sani Pantami Facebook

Yakara dacewa Babu wani laifi ko rashin dacewa don ka roki a yi following dinka, kuma duk sabbin followers din da suka yi following dinka a yanzu sune cikakkun Active Followers

 

Ga dalilaina na fadin haka;

1, Na farko Facebook babu ruwansu don ka roki a yi following dinka domin abunda suke so kenan ka tara Followers kullum ka yita hawa Online suna amfana dakai wata kila kaima ka amfana da su.

 

2, Idan kana da Followers kamar dubu 5k baka samun liking da comments da yawa to a yanzu ka dage ka kara samun followers ko da dubu 1k su zama 6k wata kila sabbin Followers dinka su dinga yi maka liking a account din naka fiye da tsoffin.

 

3, Sabbin Followers dinka na yanzu da ka samu sune ainahin cikakkun Active Followers, saboda tsoffin followers dinka wata kila da yawa daga cikinsu sun daina hawa Facebook din.

 

4, Abunda ya kamata shine da zaran ka samu sabbin Followers ka dinga kirkirar sabbin abubuwa na bidiyo da na rubutu, In Sha Allahu zaka rike sabbin Followers dinka da kyau kuma zaku karu da juna.

 

5, Matukar ka samu followers ko Facebook basu fara biyanka ba ko kadan ba kada asara domin tara followers yana da Alkhairai masu dumbin yawa duk wani Influencer da followers yake gadara.

 

6, Neman sabbin follower bazai taba sawa Facebook su maka Warning ko su baka Risk ba sai-dai idan kayi rubutun da ya sabawa dokarsu.

 

7, Masu cewa mutane, neman Followers shirmene wallahi karya suke yi, sai-dai idan wani laifi daban kayi na sabawa dokar Facebook.

 

8, Wallahi ko zuwa yanzu na tabbata dubunnan mutane ne suka samu sabbin Followers da zasu amfana da juna hakan ma babbar Nasara ce a garemu.

 

9, Samun 10K followers kafin January abune mai matukar wahala, amma idan kuka cire hassada kuka yi following din juna inada yakinin da yawa daga cikinku za su haura fiye da 10k followers.

 

10, Duk wani Influencer a Najeriya, wallahi da Followers yake gadara, da Followers yake takama. Abi duk wata hanyar da bata sabawa doka ba don a nemi Followers, domin followers sune social media.

 

LABARAI MASU ALAKA: Followers A Facebook Da Taimakon Juna Wajen Tara Followers A Facebook cewar Sadiq Rabi’u Ahmad.

 

Mallaki gidauniyar Hausa Hazaka Sadiq Rabi’u Ahmad, shima ya bayyana haka ne a farfajiyarsa na kafar ta sada zumunta inda yake cewa “Facebook da sauran dandalin sada zumunta sun zama manyan hanyoyin da ake amfani da su wajen sadarwa, kasuwanci, fadakarwa, da kuma nishadi. Tara followers a Facebook yana da matukar mahimmanci, musamman idan ana son samun tasiri, inganta kasuwanci, da kuma isar da saƙo ga mutane da yawa.

 

Mahimmancin Tara Followers

 

Isar da Saƙo cikin Sauƙi: Followers suna ba ka damar yada saƙonka ga dimbin mutane cikin gaggawa.

 

Tallata Kasuwanci: A yau, yawancin ‘yan kasuwa suna amfani da Facebook wajen tallata hajarsu, kuma babban mabuɗin nasara shine samun masu bibiyarka da yawa.

 

Samun Kudi: Duk wanda ke da mabiya da yawa yana iya juya wannan damar zuwa samun kudade ta hanyar tallace-tallace ko haɗin gwiwa da kamfanoni.

 

Matsalar Raina Ci Gaban Wasu

 

A yayin da wasu ke kokarin tara followers domin su ma su cimma burinsu, akwai wani yanayi da ake fuskanta daga wasu da suka rigaya sun tara nasu. Wadannan mutanen suna ganin babu wanda ya kamata ya kai matsayin su, suna amfani da maganganu ko wani salo na tauye ci gaban masu tasowa.

 

Abin takaici ne cewa, maimakon taimakon junanmu, muna ganin wasu suna yi wa juna kafar angulu, suna tsoron kada wani ya cimma nasara fiye da su. Wannan matsala ta fi tsanani a Arewacin Najeriya, inda muke rasa hadin kan da zai kawo mana ci gaba.

 

Darasi daga Yan Kudancin Najeriya

 

Idan muka dubi ‘yan Kudu, za mu fahimci cewa suna gina kansu da taimakon junansu ta hanyar sada zumunta. Wannan ya sanya su fi karfi a fannin amfani da social media wajen samun kudi da ci gaba.

 

Taimakon Juna: ‘Yan Kudu suna gina junansu ta hanyar taimakon juna wajen samun followers. Maimakon su tauye ci gaban wani, suna goya masa baya har ya cimma nasararsa.

 

Suna amfani da dandamali don tallata kayayyakin junansu, kuma duk wanda ya sami nasara yana jawo wasu zuwa gaba.

 

Samun Kudade: Ta hanyar wannan hadin kai, suna amfani da mabiya wajen samar da kudi da tallata kasuwancinsu, har ma da samun damar yin aiki tare da kamfanoni da ke bukatar masu tasiri a kafafen sada zumunta.

 

Abin Da Ya Kamata Mu Yi

 

Mu Zama Masu Hadin Kai: Arewacin Najeriya na bukatar koyon wannan dabi’ar daga ‘yan Kudu. Dole ne mu rinka tallafawa juna, musamman wajen tara followers, domin hakan zai amfanemu baki daya.

 

Mu Guje wa Hassada: Mu fahimci cewa nasarar wani ba ta hana taka ba, sai ma ta kara maka damar koyo da tasiri.

 

Mu zama Jagora: Duk wanda ya rigaya ya cimma nasara ya zama jagora wajen koya wa masu tasowa dabarun da za su taimaka musu.

 

Tara followers a Facebook da sauran kafafen sada zumunta na da muhimmanci a wannan zamani. A matsayinmu na ‘yan Arewa, ya kamata mu guji hassada da raina ci gaban juna. Mu koyi darasi daga ‘yan Kudu, sukan taimaka wa junansu har su kai ga samun kudade da ci gaba ta hanyar followers. Mu tuna cewa duniya tana da wuri ga kowa, kuma ci gaban wani zai iya zama dama garemu mu ma mu taso. Hadin kai shi ne mabuɗin nasara!

 

LABARI: Mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ya ziyarci Raudar Manzon Allah S.A.W 2024


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button