HISBA Karkashin Hukumar Shari’ar Musulunci na jihar Bauchi sun ziyarci kwata 2024
Hukumar Hisba a jihar Bauchi dake Arewa Maso Gabashin Najeriya ta kai ziyaran musamman kwata wajen da ake aikin yanka Dabbobi domin ganin yanda ake gudanar da aikin yanka Dabbobi a jihar Bauchi
Hukumar tayi nasiha ga masu yankan, kan kiyaye ka’idojin addinin Muslunci wajen kyautata yanka ma Dabbobi da kuma tabbatar da Lafiyar su kafin a yanka a jihar ta Bauchi.
Anyi tattaunawa mai zurfi tsakanin Hukumar Hisba ta jihar Bauchi da shugabanin kwatan kan yanda ayyukan suke gudana.
Kafar watsa labarai ta Labari daga Bauchi ne ta wallafa rahoto a shafinta na face
Dokar Haraji: Matakan amincewa da ƙudurin doka a Najeriya
LABARAI MASU ALAKA:
Ko Kuna Da Korafi Kan Yanda Ake Yanka Kaji Da Gyara Kaji A Kasuwanni A Jihar Bauchi
Kasantuwan Addinin Muslunci Bai bar komai ba sai da yayi magana kan yanda za’ayi shi.
Hukumar Hisba a jihar Bauch Karkashin hukumar Shari’ar musulunci na jihar sun ziyarci kasuwa Muda Lawan Market Bauchi bangaren yan kaji Domin tunatar da su kan yanda addinin Muslunci ya sanya sharadi kan Yankan Dabbobi wanda idan an yanka dai dai bisa Shari’a to shine yake Halatta . Musulmi su ci Nama aka sin haka kuma ya saba ma Shari’a.
Kamar yadda shugaban hukumar Hisba Barrister Aminu Balarabe Isah Esq yayi jawabi matsayin tunatarwa kan hakan.
Ko Kuma Kuna Da Korafi Kan Yanda Ake Yanka Kaji Me Ye Shawarar Ku Ga Hisba.