Hukumar EFCC ta kama wasu masu damfarar crypto 792 cikin kwana guda a Legas jihar Legas
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta yi nasarar kama wasu mutane 792 da ake zargi da damfarar a harkar crypto a jihar Legas
Da yake magana da manema labarai a ranar Litinin, kakakin hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren, ya ce an kama mutanen ne a wani gidan sama mai hawa bakwai da ke Victoria Island, a jihar ta Legas.
Uwujaren ya ce wadanda ake zargin sun hada da ‘yan China 114, ‘yan kasar Philippines 40, da Khazartan biyu, daya dan Pakistan, da kuma dan Indonesia daya kamar yadda jaridar Tribune Online Newspaper ta tabbatar.
LABARAI MASU ALAKA: Hedikwatar tsaro ta musanta kafa sansanin sojin Faransa a Najeriya 2024
Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce babu gaskiya a labaran da ake yaɗawa cewa dakarun Faransa na shirin kafa sansaninsu a Najeriya.
Wata sanarwar da daraktan yaɗa labaran Hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar a yau Litinin ta ce labaran jita-jita ce, kuma basu da tushe kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa ta Wallafa.
Ya ce, “An ankarar da hedikwatar tsaron Najeriya a kan rahotannin da ake yaɗawa a shafuka sada zumunta da ke zargin cewa zangon farko na dakarun Faransa ya isoa Maiduguri a shirye-shirye kafa sansanin su a yanki Arewa maso gabashin Najeriya.
“Rundunar sojin Najeriya na tabbatar da cewa wannan rahoto na ƙarya ne kuma bashi da makama. Idan za a iya tunawa babban hafsan Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi bayani game da wannan batu, kuma ya jaddada cewa jita-jita ne kawai aka kitsa a wannan labari.”
Hedikwatar tsaron ta buƙaci jama’a su yi watsi da rahotannin ƙaryar, waɗanda ta ce har yanzu akwai masu ci gaba da yaɗa su domin cimma muradun su na son rai.