Jagoran Kwankwasiyya ya Ziyarci Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo A Abeokuta 2024
Sanata Kwankwaso ya ziyarci tsohon shugaban kasar ne a gidansa dake abe kuta a satin da muke ban kwana dashi.
Jagoran Kwankwasiyya Naƙasa Sen. Rabiu Musa Kwankwaso, tare da abokinsa na kusa daTsohon Gwamnan Jihar Cross River , His Excellency Donald Duke, sun ziyarci Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a gidansa dake Abeokuta.
Ya bayyana wannan ziyarar amatsyi ziyara ta girmamawa wadda ta samu halartar wasu manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki na kasar nan da kuma ɗarikar Kwankwasiyya.
A yayin wannan taron, an yi muhawara kan batutuwan da suka shafi ci gaban Najeriya, musamman ma batutuwan siyasa da gwamnatoci masu ci a wannan zamanin nan, An jaddada muhimmancin haɗin kai da dimokaradiyya wajen inganta Najeriya
Taron ya bayyana irin goyon bayan da kowanne daga cikin su ke bayarwa wajen samar da mafita ga matsalolin da kasar ke fuskanta a wannan lokaci mu san man shi jagoran darikar Kwankwasiyya Dr. Rabi’u Kwankwaso.
Wannan baya ne sun fitone daga bakin Ambassador Nura Nitel kamar yadda ya bayyana a shafin sa na Facebook.
LABARAI MASU ALAKA: Zan kawo sauyi mai ma’ana a Najeriya cewar sanata Kwankwaso 2024
Jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana tsantsar burinsa na ganin Najeriya ta samu cigaba mai ɗorewa. a shekarar 2027, ya yi alkawarin
Jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana tsantsar burinsa na ganin Najeriya ta samu cigaba mai ɗorewa. a shekarar 2027, ya yi alkawarin
1. MAGANCE YUNWA DA TALAUCI
Kwankwaso ya sha alwashin kawo sabbin tsare-tsare da za su magance matsalar talauci, haɓaka aikin yi, da tallafa wa marasa galihu domin rage radadin wahala a ƙasa. Kamar yadda zinariya ta ruwaito.
2. DAWO DA MARTABAR NAJERIYA
Ya ce lokaci ya yi da za a dawo da kimar Najeriya ta hanyar shugabanci nagari da ƙwarai wanda zai ba kowanne ɗan ƙasa damar alfahari da ƙasar.
3. HAƁAKA TATTALIN ARZIKI
Jagoran ya bayyana cewa za a farfaɗo da masana’antu, noma, da kasuwanci domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da ƙirƙirar hanyoyin dogaro da kai.
4. SAKE FASALIN NAJERIYA
Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin samar da gaskiya, tsaro, da zaman lafiya ta hanyar gyara tsarin shugabanci domin kowa ya ji daɗin rayuwa.
“Na yi imani da Najeriya. Tare da haɗin kanmu, zan jagoranci ƙasar nan zuwa ga ingantacciyar makoma a shekarar 2027.” – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.