KANO: AMB. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya gargaɗi Alhaji Abdullahi Abbas 2024

Ogan Boye Ya Gargadi Shugaban Jam'iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas tare da Baffa Babba dan agundi da Alhassan Ado Doguwa

Spread the love

Shugaban Ƙaramar Hukumar Nassarawa Amb. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya gargaɗi Shugaban Jam’iyyar APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas kan sukar tsarin tafiyar Gwamnatin Kwankwasiyya.

KANO: AMB. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya gargaɗi Alhaji Abdullahi Abbas 2024
Ogan ɓoye

A hirarsa da manema labarai Ogan Ɓoye ya bayyana Abdullahi Abbas ɗin a matsayin farar Kura wanda ba ya iya kataɓus a siyasa sai dai iya fatar baki.

 

Da yake martani ga Baffa Babba kuwa Ogan Ɓoye ya ce yana sanar masa cewa ƙaryarsa ta sha ƙarya a siyasa domin ƴan Kwankwasiyyar ba kanwar lasa bane don haka ya fita a idonsu.

 

Game da kalaman Alhassan Ado Doguwa na baya-bayan nan kuwa Ogan Ɓoye ya ce sun shirya lakace hancin Doguwan a siyasance matuƙar ya ci gaba da sukar Engr. Rabi’u Kwankwaso.

 

Ogan Ɓoye ya nemi ƴan APCn Kano su sani cewa yanzu zamani ne na Kwankwasiyya kuma ba za su ɗauki nuna rashin ta ido ga Gwamnatinsu ba.

 

LABARI MASU ALAKA: Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya sanar da gyare-gyare a majalisar zartarwar jihar, inda ya cire wasu, sannan ya sauya wa wasu ma’aikatu.

 

A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya soke ofishin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, wanda Alhaji Shehu Wada Sagagi ke riƙewa, sannan ya cire sakataren gwamnatin jihar, Dokta Baffa Bichi saboda rashin lafiya.

 

Sanarwar ta ce gwamnan ya cire kwamishinoni guda biyar: Ibrahim Jibril Fagge na ma’aikatar kuɗi da Ladidi Ibrahim Garko ta ma’aikatar al’adu da yawon buɗe ido da Baba Halilu Dantiye na ma’aikatar watsa labarai da Shehu Aliyu Yammedi na ma’aikatar ayyuka na musamman da Abbas Sani Abbas na ma’aikatar raya karkara.

 

Sanarwar ta ce gwamnan ya yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati, da kuma taimaka wa gwamnan wajen kai romon dimokuraɗiyya ga ƴan jihar Kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa ta ruwaito.

Muhimman sauye sauye shida da za a yi wa tsarin zaɓen Najeriya INEC 2024

Muhimman sauye-sauye shida da za a yi wa tsarin zaɓen Najeriya INEC
INEC

Haka kuma gwamnan ya yi wa wasu kwamishinonin sauyin ma’aikatu, waɗanda suka haɗa da: “mataimakin gwamnan jihar, wanda aka sauya masa ma’aikata daga ƙananan hukumomi zuwa ma’aikatar ilimi mai zurfi, da Mohammad Tajo Usman daga ma’aikatar kimiyya da fasaha zuwa ma’aikatar ƙananan hukumomi, da Dr Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata daga m’aikatar ilimi mai zurfi zuwa kimiyya da fasaha.”

 

Sauran sun haɗa: “Hajiya Amina Abdullahi daga ma’aikatar jinƙai da rage talauci zuwa ma’aikatar mata, da Nasiru Sule Garo daga ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman da Haruna Doguwa daga ma’aikatar ilimi zuwa ma’aikatar albarkatun ruwa da Ali Haruna Makoda daga ma’aikatar albarkatun ruwa zuwa ma’aikatar ilimi da Aisha Lawal Saji da aka mayar m’aikatar al’adu da yawon buɗe ido.”

 

Sai dai gwamnan ya buƙaci waɗanda aka cire ɗin su je ofishinsa domin a ba su wasu ayyukan daban.


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button