KOYAN AIKIN ZABE: Jami’an zabe na Jamhuriyar Benin sun ziyarci INEC don koyon aiki 2024

Wata tawaga mai mambobi 12 daga Hukumar Zaɓe Mai Cin Gashin Kanta ta Jamhuriyar Benin (CENA) ta ziyarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a wata ziyarar neman karin sani.

Spread the love

Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Sacca Lafia, shugaban CENA, ta ƙunshi kwamishinonin ƙasa, direktoci, da manyan ma’aikata.

https://dailynewshausa.com/?p=226&preview=true zabe

The able ta ruwaito cewa an tarbi tawagar a ranar Litinin daga Mahmood Yakubu, shugaban INEC, tare da sauran mambobin hukumar a hedkwatar INEC da ke Abuja.

 

A cewar Lafia, manufar ziyarar ita ce domin koyon darussa daga tsarin zaɓen Najeriya da kyawawan ayyukanta, yayin da Jamhuriyar Benin ke shirin gudanar da zaɓen ta na 2026 mai zuwa.

 

Da yake jawabi a taron, Yakubu ya jaddada muhimmancin wannan ziyara da kuma ƙalubalen da CENA ke fuskanta kafin zaɓen.

 

“Farkon watan da ya gabata, mun karɓi wasiƙa daga CENA da ke nuna sha’awar su ta yin wata ziyarar karatu zuwa INEC Najeriya yayin da suke shirin gudanar da abin da suka kira mafi rikitarwa daga cikin zabukan su a shekarar 2026,” in ji shi.

LABARAI MASU ALAKA: Hukumar zaɓe a Najeriya INEC, ta yi watsi da rahotanni da ake yayatawa kan mutuwar shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu.

 

Hukumar zaɓe a Najeriya INEC, ta yi watsi da rahotanni da ake yayatawa kan mutuwar shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu.

 

iƙirarin cewa shugaban hukumar zaɓen Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu ya mutu a wani asibiti a birnin Landan. Wannan ba gaskiya bane,” in ji sanarwar.

 

Sanarwar ta ce mutane su yi watsi da labarin mutuwar shugaban na INEC, inda ta ce yana cikin koshin lafiya, kuma bai ma yi wata tafiya zuwa birnin Landan ba a cikin shekaru biyu da suka wuce.

 

An dai fara yayata batun mutuwar Farfesa Yakubu a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba a kan kafofin sada zumunta.

 

Sai dai INEC ta ce shugaban nata ya ma halarci wani zama da kwamitin majalisar wakilai kan ɓangaren zaɓe ranar Laraba, 11 ga Disamban 2024.

Najeriya

 

INA NAN DA RAINA SHUGABAN INEC: Sanarwar ta kuma bayyana cewa Farfesa Yakubu ya halarci wani taron mu’amala tare da Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Zabe a ranar Laraba, 11 ga Disamba, kamar yadda jaridar VOA Hausa  ta Wallafa.

 

KOYAN AIKIN ZABE: Jami’an zabe na Jamhuriyar Benin sun ziyarci INEC don koyon aiki 2024

Shugaban Hukumar zabe ta INEC a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce yana nan da ransa.

 

An yi ta ramadidin cewa shugaban hukumar ta INEC ya rasu a ‘yan kwanakin nan.

 

Sai dai cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Rotimi Oyekanmi ya fitar, Yakubu ya ce yana nan da ransa.

 

“An jawo hankalinmu kan wani labari na kmara tushe da aka yada a wasu sassan kafafen sada zumunta, inda aka yi ikirarin cewa shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya mutu a wani asibiti a London. Labarin ya fara bayyana ne a ranar Litinin, 9 ga Disamba, 2024.”

 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Farfesa Yakubu ya halarci wani taron mu’amala tare da Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Zabe a ranar Laraba, 11 ga Disamba, 2024.

 

Haka kuma, ya jagoranci taron Hukumar tare da Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi a ranar Alhamis, 12 ga Disamba, 2024.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button