Ma’aikata 9,500 Suna Neman A Biya Su Albashinsu Na Watanni Biyu A Jihar Adamawa

Ma'aikatan jihar Adamawa sun koka kan rashin samun albashin su na watan nowamba da kuma wannan watan da muke ciki.

Spread the love

Ma’aikata 9,500 Suna Neman A Biya Su Albashinsu Na Watanni Ba’aikatan suna cigaba da koka wa musamman malaman makarantar gaba da piramari kan rashin biyansu haƙƙoƙinsu na albashi da gomnati ta gagara biyan su bayan sun cika sharuda da gomnati ta ayyana musu.

 

https://dailynewshausa.com/?p=254&preview=true Adamawa

A kwanakin baya ne gomnati jihar Adamawa ta zargi wasu ma’aikatan ta da yin amfani da takardun boge a lokacin da aka dauke su aiki, wanda haka ya sa ta fito da wani tsari domin tan-tance zare da a bawa.

 

Gomnati Jihar Adamawa ta bawa ma’aikatan ta mako uku domin su bayyana takardun su na gaskiya da aka dauke su aiki domin tan-tance su, wanda tuni ma’aikatan suka mika mata takardun kamar yadda ta bukata, sai dai an samu kadan da basu mika ba saboda rashin gaskiya.

 

Wani ma’aikaci a jihar ya shaidawa jaridar Rariya cewa duk wasu matakan da gomnati jihar ta fito dasu domin tan-tance ma’aikatan sun cika wadan nan ka’idodin, kuma daga cikin ma’aikatan akwai wadan da sun mika takardun shedar karatun su da aka dauke su aiki dashi ya kai sau uku amma ba’a biya su albashin su na watanni biyu ba.

 

” Hakika mun shiga cikin wani hali sanadiyyar rashin samun albashin mu, wanda hakan ya kai ga koran yaran mu daga makaranta sabida rashin kudin makaranta, ga halin da kasa ke ciki na tsadar rayuwa, hakika wannan babban kalubale ne a garemu”.

 

Haka zalika gomnati jihar tayi amai ta lashe kan batun mafi karanci albashi da ta fara biya da kaso 100, daga bisa ni kuma ta zaftare kaso mai tsoka daga ciki, zuwa yanzu haka ko wanne ma’aikaci an zaftare masa 9,000 daga cikin abinda gomnatin ta kara a watan ugustan da ya gabata.

Daga karshe muna kira ga gomnatin jihar Adamawa karkashin jagoranci Ahmadu Umaru Fintiri data tausaya mana ta ta biya mu hakkonkin mu mu samu na bukin kirsimeti.

 

LABARI: Babu wani laifi ko rashin dacewa don ka roki a yi following dinka a Facebook – Comr Abba Sani Pantami 2024


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button