Mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ya ziyarci Raudar Manzon Allah S.A.W 2024
Shettima ya ziyarci Raudar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama dake garin Madina.
A wata ziyarar Ibada da yakai a Kasa mai Tsarki, mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima ya fara yada zango a Raudhah, wato makwancin Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad SALLALLAHU ALAIHI WA ALIHI WASALLAM, da ke tsakanin gidansa da Masallacinsa a garin Madinatul Munawwara dake kasar Saudiya.
Kashim Shettima ya isa wajen tare da rakiyar gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, da Engr Ibrahim Umar na Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya; da jami’an Ofishin Jakadancin Najeriya a Saudiyya,
Mataimakin Shugaban kasar Shettima ya yi addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da bunkasar arziki ga Nijeriya, da ma duniya baki daya.
Haka zalika Mataimakin shugaban kasar Shettima ya ja hankalin duniya da wannan ziyara ta wuri mai dauke da tsarki da tarihi a Musulunci, inda ya saje da dubban musulmi wajen neman yardar Allah da Salati ga Manzon Allah SALLALLAHU ALAIHI wasallam.
Da yake jawabi bayan kammala ziyarar mai cike da tarihi da ibada, mataimakin shugaban kasar ya bayyana jin dadinsa dangane da samun damar ziyartar wannan wuri mai tarin albarka, dake kunshe da lada da kuma koyarwar Annabi Muhammad (SAWA) wannan wuri, daya ne daga wurare biyu da miliyoyin Musulmi masu neman kusanci da Ubangiji, da aminci, ke dafifin zuwa ziyara.
Kamar yadda Rahma Abdulmajid ta Wallafa a shafin ta na facebook.
RAHOTO: Hukumar EFCC ta kama wasu masu damfarar crypto 792 cikin kwana guda a Legas jihar Legas
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta yi nasarar kama wasu mutane 792 da ake zargi da damfarar a harkar crypto a jihar Legas
Uwujaren ya ce wadanda ake zargin sun hada da ‘yan China 114, ‘yan kasar Philippines 40, da Khazartan biyu, daya dan Pakistan, da kuma dan Indonesia daya kamar yadda jaridar Tribune Online Newspaper ta tabbatar.