Matawalle Ya Jagoranci Taron Kaddamar Da Hukumar DICON Domin Bunkasa Samar Da Makamai A Cikin Gida 2024
Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya, Dr Bello Muhammad Matawalle, ya jagoranci taron shugabannin hukumomin kamfanonin kere-keren abubuwan da suka danganci tsaro na Nijeriya (DICON), wanda ke nuna wani muhimmin mataki na farfado da bangaren masana'antun bangaren tsaron kasar.
Taron wanda aka gudanar a ma’aikatar tsaro da ke Abuja, ya biyo bayan zartar da dokar DICON ta 2023 da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu a watan Satumbar 2023.
Dokar na da nufin sabunta ayyukan DICON da fadada ayyukanta, tare da kara kaimi ga burin Nijeriya na samun wadatuwa wajen samar kayan inganta tsaro.
DICON, wanda aka kafa a cikin 1964, yana da alhakin samar da muhimman kayan aikin soja, ciki har da kananan makamai, alburusai, da motoci masu sulke.
Taron hukumar ya tattaro manyan hafsoshin soji, da hafsoshin tsaro, da wakilai, da suka hada da na rundunar ‘yan sandan Nijeriya, domin tattauna dabarun inganta gudunmuwar da DICON ke badawa a harkokin tsaron kasa.
Da yake jawabi yayin taron, Dr. Matawalle ya jaddada babbar gudunmuwar da DICON ke badawa a fannin samar da tsaro a Nijeriya. “Duk cibiyoyin DICON dole ne su yi aiki.
Wannan ita ce babbar hanyar da za a bi wajen cimma burin dogaro da kai wajen samar da tsaro,” in ji shi. “Kokarin da muke yi na hadin guiwa zai kara karfin hukumar DICON don biyan bukatun sojojin kasar da kuma ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arziki.”
Dr Matawalle ya jaddada muhimmancin haɗin guiwa da masana’antu na cikin gida don inganta samar da ayyukan yi, rage zaman kashe wando, da kuma inganta tsaro na Nijeriya.
Ya sake jaddada kudirin gwamnatin shugaba Tinubu na tallafa wa DICON a matsayin muhimmin bangaren masana’antun kere-keren sojan Nijeriya.
Bayan kammala taron, Dr Matawalle ya duba motocin da ake kerawa na Mine-Resistant Ambush Protected (M-RAP) da kuma motocin masu sulke na (APCs) da wani kamfani mai suna E-PAIL Nigeria ke aikin kerawa.
Motocin, wanda Shugaban kamfanin E-PAIL Engr. Kola Balogun, ya nuna yadda masana’antun ‘yan asalin kasar ke ci gaba da yin hadin guiwa wajen karfafa fasahar tsaron Nijeriya.
Fadada aikin DICON a karkashin sabuwar dokar ya yi daidai da manufofin Nijeriya na rage dogaro da shigo da makamai daga kasashen waje, inganta tsaron kasa, da bunkasa masana’antu.
Ci gaban da aka samu na baya-bayan nan, kamar kera motoci masu sulke da masu ɗaukar ma’aikata, suna nuna ƙarar rawar da kamfani ke takawa a fagen inganta tsaro a nahiyar Afirka bakidaya.
Taron hukumar ya nuna wani muhimmin lokaci ga DICON yayin da yake kokarin sabunta ayyuka da kuma ba da gudummawa don dogaro da kai wajen samar da tsaro.
LABARAI MASU ALAKA: Hedikwatar tsaro ta musanta kafa sansanin sojin Faransa a Najeriya 2024
Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce babu gaskiya a labaran da ake yaɗawa cewa dakarun Faransa na shirin kafa sansaninsu a Najeriya.
Wata sanarwar da daraktan yaɗa labaran Hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar a yau Litinin ta ce labaran jita-jita ce, kuma basu da tushe kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa ta Wallafa.
Ya ce, “An ankarar da hedikwatar tsaron Najeriya a kan rahotannin da ake yaɗawa a shafuka sada zumunta da ke zargin cewa zangon farko na dakarun Faransa ya isoa Maiduguri a shirye-shirye kafa sansanin su a yanki Arewa maso gabashin Najeriya.
“Rundunar sojin Najeriya na tabbatar da cewa wannan rahoto na ƙarya ne kuma bashi da makama. Idan za a iya tunawa babban hafsan Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi bayani game da wannan batu, kuma ya jaddada cewa jita-jita ne kawai aka kitsa a wannan labari.”
Hedikwatar tsaron ta buƙaci jama’a su yi watsi da rahotannin ƙaryar, waɗanda ta ce har yanzu akwai masu ci gaba da yaɗa su domin cimma muradun su na son rai.