Rashin tsaro: Lakurawa sun tafka babban kuskure, domin babu wanda ya taba ja da Tinubu kuma ya yi nasara, inji Nuhu Ribadu

harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya ce babu wanda ya isa ya daura damara da shugaban kasa Bola Tinubu, kuma ya ci gaba da zama lafiya, ya gargadin sabuwar kungiyar ta’addanci, Lakurawa, kan kuskuren da suke ƙokarinyi na mamaye yankin arewa maso yamma

Spread the love



Rashin tsaro: Lakurawa sun tafka babban kuskure, domin babu wanda ya taba ja da Tinubu kuma ya yi nasara, inji Nuhu Ribadu



Wannan dai ya zo ne a ranar da babban hafsan tsaron kasar, CDS, Janar Christopher Musa, ya tura tawagar sojoji zuwa karamar hukumar Augie da ke jihar Kebbi da ke fama da rikici inda ‘yan kungiyar ta’adda suka kashe mutane akalla 17 a kauyen Mera.

Mallam Ribadu, ya yi magana a wajen taro a Abuja, ya sha alwashin cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin tarayya za ta kawar da kungiyar.

Hukumar NSA, wacce ta wakilci shugaban kasa a taron, ta ce: “Sabuwar kungiyar, Lakurawa, sun yi kuskure, duk yadda suke ji da kansu, zamu kawo ƙarshen su nanda karshen shekara ta 2024.

“Babu wanda ya isa yayi nasara akan Tinubu wannan kuskure sukay Babu ‘Yan ta’addan da suka kasance a sassa da dama na kasar nan, muna kashe su.

“Mun kawo karshen ƴan Neja Delta, shiru ake ji. Shi yasa Yanzu muke iya samar da ganga miliyan 1.8 a kowace rana. Haka yanta da ƙayar baya naKudu maso Gabas, suma babu labarinsu.

“A karon farko a tarihin kasarmu, daukacin shugabannin sassan tsaro suna aiki a matsayin runduna guda daya, jami’an leken asiri, ‘yan sandan farar h, da sauran su. Fiye da kowane lokaci, muna aiki a matsayin ƙungiya, a matsayin ɗaya. Kuma mun fara ganin ribar da aka samu. Abin da muke kira ribar Tinubu.

“Ana kashe daruruwan ‘yan fashi a kowace rana. Kuna tafiya ko’ina a cikin ƙasarmu a yau ba tare da tsoro ba, ribar Tinubu. Abubuwa suna canzawa.

“Wadannan wadanda ake kira Lakurawa ko duk abin da aka kira su, suna yin kuskure. Babu wanda ya kuskura Tinubu ya yi nasara, ba kowa. Sun zo a lokacin da bai dace ba. Babu wanda ya taba kayar da Tinubu. Za a ci su ne. Za mu kore ku (Lakurawa) daga Najeriya.

“Wannan Najeriya ce ta 2024. Wannan Najeriya ce inda na tabbatar muku, masu suka za su yi shiru. Daya bayan daya al’amura za su canza a kasarmu kuma sun riga sun canza.

“Yawancin sassan kasarmu a yau suna zaune lafiya. Jeka Neja Delta,A yau muna samu gangar danyen mai miliyan 1.8 a kowace rana.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button