‘Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Abia a safiyar yau Laraba

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani shingen binciken sojoji da sanyin safiyar yau Laraba a garin Ekenobizi da ke kan iyaka tsakanin jihohin Abia da Imo a Umuopara a karamar hukumar Umuahia ta Kudu, inda suka kashe sojoji biyu

Spread the love

‘Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Abia a safiyar yau Laraba

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da rundunar hadin gwiwa ta Operation Udoka ta Kudu maso Gabas ta fitar Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Laftanar Kanar Jonah Unuakhalu, tana zargi kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biyafara ta IPOB, ta Eastern Security Network, ESN da kai harin.

Awata bangaren na sanarwar tace: “Da sanyin safiyar yau (13 ga Nuwamba, 2024), an kai wa sojojin hadin gwiwa na rundunar hadin gwiwa ta Kudu maso Gabas Operation UDOKA hari a wani shingen binciken ababen hawa da ke kan titin Umuahia- Owerri a karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abia. Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da kuma reshenta masu dauke da makamai, watau Eastern Security Network (ESN).

“A lokacin sa suka kawo harin, dakarun sojojin sun yi nasarar dakile harin, Amma abun yayi ƙamari lamarin da ya tilasta wa jami’an tsaro janyewa, inda sukayiwa wasu raunukan harbin bindiga, jami’an tsaron sunyi nasarar kifar da motar Sienna daya da wata mota kirar Lexus Jeep da aka yi amfani da su wajen kai harin. Sai dai kuma a tashin hatsaniya da ta biyo baya, sojoji biyu sun biyu su rasa ransu.”

Sanarwar tana cigaba da neman bayanai da za su taimaka wa Sojoji wajen cafke maharan da suka tsere.

“Rundunar hadin gwiwa ta Kudu maso Gabas Operation UDOKA tana jan hankali tare da yin kira ga mutanen Kudu maso Gabas, musamman mazauna jihar Abia, da su sanar da ita duk wani motsin ayyukan kungiyar dabasu gane ba.

“Rundunar hadin gwiwa ta Kudu Maso Gabas Operation UDO KA za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta kamar yadda tsarin mulki ya tanadar na kare rayuka da dukiyoyin Al’umma.
‘Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Abia a safiyar yau Laraba


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button