Yan Sanda jihar Gombe sun kama wasu matasa da ake zarkinsu da aikata lafin fashi da makami

Rundunar Yan Sanda jihar Gombe tayi nasarar kama wasu matasa da ake zarkinsu da aikata lafin fashi da makami.

Spread the love

Matasan masu Suna Abubakar Musa 22yrs da Usman Ismail 20yrs dake unguwar Nasarawo Gombe State.

Ankamasu da adda da takobi inda suka farwa mutanen da basuji basu ganiba harma suka rabasu da wasu daga cikin mahimman kayayyakinsu, dasuka hada da wayoyin hannu wato (handsets) Wanda kimar kudinsu takai Dubu dari shida da daya ₦601,000.

Rundunar Yan Sanda tana Kara Kira ga jama’a dasu Kula tare da mika korafinsu zuwa hukumar Yan Sanda mafi kusa kuma Akan lokaci.

Tun abaya hukumar yan sandan ta kara tsaurara tsaro ne Lokacin da tasamu sabon Kwamishinan yan sandar jihar CP Hayatu Usman.

Sanarwar ta fito ne ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ASP Buhari Abdullahi.

Jami’in Hulda da jama’a na Rundunar Yan Sanda jihar Gombe ya tabbatar da aukuwar lamarin ne lokacin da suke baje kolinsu a helkwatartar yan sandan jihar ta Gombe.

Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button