Zan kawo sauyi mai ma’ana a Najeriya cewar sanata Kwankwaso 2024
Jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana tsantsar burinsa na ganin Najeriya ta samu cigaba mai ɗorewa. a shekarar 2027, ya yi alkawarin
Jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana tsantsar burinsa na ganin Najeriya ta samu cigaba mai ɗorewa. a shekarar 2027, ya yi alkawarin
1. MAGANCE YUNWA DA TALAUCI
Kwankwaso ya sha alwashin kawo sabbin tsare-tsare da za su magance matsalar talauci, haɓaka aikin yi, da tallafa wa marasa galihu domin rage radadin wahala a ƙasa. Kamar yadda zinariya ta ruwaito.
2. DAWO DA MARTABAR NAJERIYA
Ya ce lokaci ya yi da za a dawo da kimar Najeriya ta hanyar shugabanci nagari da ƙwarai wanda zai ba kowanne ɗan ƙasa damar alfahari da ƙasar.
3. HAƁAKA TATTALIN ARZIKI
Jagoran ya bayyana cewa za a farfaɗo da masana’antu, noma, da kasuwanci domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da ƙirƙirar hanyoyin dogaro da kai.
4. SAKE FASALIN NAJERIYA
Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin samar da gaskiya, tsaro, da zaman lafiya ta hanyar gyara tsarin shugabanci domin kowa ya ji daɗin rayuwa.
“Na yi imani da Najeriya. Tare da haɗin kanmu, zan jagoranci ƙasar nan zuwa ga ingantacciyar makoma a shekarar 2027.” – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Yahaya Bello a yau juma’a
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan kuɗi naira miliyan 500.
A zaman da kotun ta yi a yau Juma’a ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Emeka Nwite, kotun ta buƙaci ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa domin samun belin.
Alƙalin ya ce dole ne mutanen da za su tsaya masa su kasance sun mallaki kadarori a Abuja, babban birnin ƙasar kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa Ta Ruwaito.
Haka kuma kotun ta ce dole ne masu tsaya masan su gabatar wakotun takardun kadarorin nasu domin tantancewa.
A baya-bayan nan ne dai hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gurfanar da tsohon gwamnan na Kogi a gaban kotu bisa zarge-zarge 19 da suka ƙunshi almundahanar kuɗaɗe da yawansu ya kai naira biliyan 80.
Lamarin da ya sa kotun ta tura shi gidan gyaran hali, a yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar.
Sai dai Yahaya Bello ya musanta aikata ba daidai ba.
Mai shari’a Nwite ya ce dole ne tsohon gwamnan ya ajiye wa fasfo ɗinsa n tafiye-tafiye.
Haka kuma ya bayar da umarnin ci gaba da tsare shi a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da zai cika sharuɗan beli.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai babbar kotun Abuja ta tura tsohon gwamnan gidan yarin Kuje bayan fatali da buƙatar belinsa kan zarge-zargen karkartar da sama da naira biliyan 100 a lokacin da yake gwamnan jihar da ke tsakiyar Najeriya.
https://www.bbc.com/hausa/live/c5yvlnl03nyt
LABARI MAI ALAKA: Ko Aranar Ta Talatan data gabata kotun ta dage zamanta zuwa 29 ga watan Janairu da 27 na watan Febrairun 2025 domin cigaba da sauraron karar.
Babbar kotun birnin tarayyar Najeriya Abuja ta bada ajiyar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a gidan gyaran hali na Kuje kafin ta saurari bukatar neman belinsa.
Haka kuma kotun ta dage zamanta zuwa 29 ga watan Janairu da 27 na watan Febrairun 2025 domin cigaba da sauraron karar.
Mai Shari’a Maryam Anenih taki amincewa da bukatar neman belin da Yahaya Bello ya shigar, inda tace an gabatar da ita da wuri.
Bello ya shigar da bukatar neman belin ne a ranar 22 ga watan Nuwamban daya gabata amma sai a ranar 26 ga watan aka tsare shi sannan aka gurfanar da shi a kotu a ranar 27.
Tsohon gwamnan na fuskantar tuhuma tare da wadansu mutane 2, akan zargin halasta kudaden haram har Naira bilyan 110 da hukumar efcc mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ke yi masa.